21 Yuli 2020 - 12:58
Iraqi: An Kama Wani Kwamnadan Mayakan Daesh A Gabacin Kasar

Wata majiyar jami’an tsaron kasar Iraqi ta bayyana an kama wani kwamanda na mayakan Daesh a lardin Diyala da ke gabacin kasar.

ABNA24: Kamfanin dillancin labaran “Shafaq News” ya nakalto Fathul Azawi kwamandan runduna ta “Nida Diyala” yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa an kama kwamandan kungiyar ta Daesh da wasu mayakan kungiyar ne a yankin “Sansanin A’isha” da yake kan tuddan “Hamraini”na lardin na Diyala.

Labarin ya kara da cewa har yanzun kungiyar ta Daesh tana da wasu sansanoni a kan iyakar Lardin Kirkuk da kuma gabacin lardin Diyala. Don haka ne dakarun Hashadushaabi da kuma taimakon sauran bangarorin jami’an tsaron suke kokaron ganin an share wadannan sansanoni.

342/